Connect with us

News

Kungiyar Vision Spring Da Tallafin M’G’E Medical Store Sun Yiwa Masu Fama Da Larurar Ido Gwaji Kyauta

Published

on

IMG 20240921 WA0024

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kungiyar Vision Spring  dake Karkashin kulawar  EHA CLINIC tare da tallafin M G E Medical Store sunyiwa Al’umma masu larurar gani sama da Mutane 300 gwajin Ido Kyauta tare da basu magangunan da zasu ruga amfani dasu dan magan ce matsalolinsu.

Advertisement

 

 

Advertisement

Kungiyar tayi wannan taron gwajin Idon ne a ranar Alhamis a harabar Babban Shagon MGE dake Unguwar Tudun Yola Gate Five 5.

Badaƙalar Filaye:  Hukumar Shari’a Ta Dakatar Da Ma’aikatan Kotu A Kano

Shugaban M’G’E Medical Store Yunusa Musa Rabiu dake da Kwarewa a fannin hada magunguna  da Kuma sanin cututtuka masu yaduwa  ya ce kungiyar Vision Spring tayi wannan gwajin Idon Kyauta ne domin baiwa Al’umma masu Larurar damar fadin abinda yake damunsu musamman ma Mutanen da Shekarunsu suka haura 35.

Advertisement

Sannan kuma masanin ya Kara da cewa bayan sunyi gwaji kyauta suna duba irin matsalar da mutum yake da ita sannan su dorashi akan magani.

Bayan kwajin kyauta kuma kungiyar Vision Spring tayi ragin kaso Tamanin 80 cikin Dari 100 ga wadan gwajin ya nuna Gilashi za’abasu ko kuma magani.

Advertisement

Yunusa Musa Rabiu ya ce wannan shine Karan farko da Vision Spring ta duba masu matsalar gani a Unguwar ta Tudun Yola kuma nan bada jimawaba kungiyar zata dawo domin sake duba wasu masu neman lafiya.

A nasa jawabin shima Mai Unguwar Tudun Yola Malan Kabir Shehu Abdullahi ya nuna matukar jin daɗinsa na Yadda wannan kungiyar ta baiwa Al’umma yankinsa kulawa sannan ya ce zasu bada kowacce irin gudunmawa akan irin wadannnan ayyukan Alkhairi ga kowacce irin kungiya

Advertisement

 

Sannan kuma mai Unguwar ya bukaci daukacin Al, umma dasu fito nan gaba idan har idan za’a kara irin wannan aikin alkhairin

Advertisement

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa jama’ar da akayiwa wannan gwajin sun nuna matukar jin daɗinsu tare da Yiwa Wadanda sukayi wannan Aiki Fatan alkhairi.

 

Advertisement

Kungiyar Vision Spring dake zaune a independent road kungiya ce data Shahara wajen  aika ce aika ce alkhairi da dama da suka shafi lafiyar jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending