Connect with us

News

Kaso 60 Na Al’ummar Najeriya Suna Rayuwa A Cikin Kangin Talauci —Peter Obi

Published

on

Kaso 60 na al’ummar Nigeria suna rayuwa a cikin talauci–Peter Obi
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar LP, a zaben shekarar 2023 Peter Obi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar LP, a zaben shekarar 2023 Peter Obi, ya ce ayyukan ta’addanci da suka addabi kasashen nahiyar Africa sun tilastawa al’ummar yankin fadawa cikin kangin talauci.

Peter Obi ya bayyana hakan a lokacin daya halarci wani taron daya kunshi manyan shugabanni da jagororin kasashen duniya don tattaunawa akan shugabanci na gari a nahiyar Africa.

Mummunar Gobara Ta Babbake Motar Makaranta Tare Da Hallaka Fiye Da Yara 20

Inda ya zayyano cewa rashin aikin yi, cin hanci da rashawa, nuna banbanci, na daga cikin dalilan da suka hana yankin nahiyar  Afrika zama cikin kwanciyar hankali da luman.

Daily News24 ta ruwaito cewa taron ya hadar da manyan jami’an gwamnati, jami’an tsaro, masana harkokin wasanni, da tsaffin sojoji, an kuma tattauna akan kalubalen da fannin tsaro ke ciki da tattalin arziki sai Kuma hasashen yanayin da za’a iya samun kai a ciki nan gab

Pater Obi, yace a matsayin su na jagororin al’umma dole ne su yi kokarin kawo wa mutane mafita daga halin kuncin rayuwa da ake fuskanta a yanzu da wanda ake hasashen samu nan gab

Advertisement

Tsohon gwamnan jihar ta Anambra, ya bayyana hakan a yau asabar ta hannun kakakin sa Ibrahim Uma

Daga cikin matakan da yace akwai bukatar a dauka don shawo kan matsalolin da Afrika ke ciki akwai kakkabe talauci, magance rashin adalci, ta dakile nuna wariya a tsakanin al’umm

Sannan yace kaso 50 cikin dari na masu fama da talauci a duniya yan nahiyar Africa ne, inda ya kara da cewa kaso 60 cikin dari na al’ummar kasashen Najeriya da Congo suna yin rayuwa a cikin kuncin talauci

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending