News
Hukumar Hisbah Ta Sake Gano Wani Gida Da Aka Mai Dashi Na ‘Sheƙe Aya A Kano
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta samu Nasarar kama wani matashi da aka gano wata jaka mai dauke da kayan yara wadda aka zubo Miya gun Kwayoyi a ciki ana turowa daga Legos shi kuma ya tura Adamawa
Mujahid Aminudeen mataimakin shugaban Hisbah ne ya baiyyana hakan a cikin wani sakon Murya da ya turawa da Jaridar INDA RANKA
Sanatocin Arewacin Najeriya 12 Da Suka Gaza Gabatar Da Ƙudiri A Watanni 15 — Rahoto
Aminudeen ya kara da cewa yanzu haka kayan yana hunnun hukumar hisbah ana bincike akai yadda za a gano mai turo da kayan da wanda ake turawa
Haka kuma Hukumar hisbah ta sake gano wani gida a unguwar panshekara wanda mai gidan ya mai dashi lojan an chafke mai gidan da mutannan da aka samu a gidan
Aminudeen ya ce jami’ansu zasu bazu a lungu da sakon Jihar Kano domin tabbatar da bin dokokin da gwamnatin Kano ta kafa na yaki da lalata tarbiyyar al’umma.
Sun kuma bukaci al’umma da su rika kawo rahoton wuraren da ake gudanar da abubuwan da ba su dace ba, domin kare mutuncin jihar Kano da kuma addinin muslinci don gujewa fadawa cikin fishin Ubangiji.
