News
Matsin Rayuwa: Yakamata gwamnatin tarayya ki tausayawa al’umma a rage farashin Fetur – Human Right
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙungiyar kare hakƙin ɗan adam ta Sustainable Growth Initiatives for Human Right Development, ta ƙalubalanci gwamnatin tarayya kan yadda take ta yiwa ƴan ƙasa ƙarin farashin man fetur, duk kuwa da halin tsadar rayuwar da suke ciki.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Abubakar Musa Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai ranar Lahadi a Kano.
Dalibai Maza Sun Fi Mata Yawan Satar Amsa A Lokacin Jarrabawa
Kwamared Abubakar Musa ya ce yadda al’ummar ƙasa suke ci gaba da fuskantar halin matsin rayuwa, bai kamata gwamnati ta saka musu da musguna musu ta bangarori daban-daban ba wanda hakan ke ƙara jefa su cikin damuwa.
“Daga lokacin da kuɗin man fetur ya nunka to komai ma ninkawa yake yi wanda harkokin kasuwanci, da cin Abinci ga mutane, da sauran buƙatu duk suka ɗai-ɗai ce, a don haka ya kamata Sanatoci, da Ƴan Majalisar Wakilai, da gwamnoni, da dukkanin masu ruwa da tsaki ku yi abinda ya dace domin ganin al’umma sun samu sauƙi, “in ji Abubakar”.
Daraktan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin ya kuma ƙara da cewar ya kamata suma malamai su tashi haiƙan wajen faɗawa shugabanni gaskiya, wajen ganin sun tausayawa al’umma domin samun mafita daga tsadar rayuwar da suke ciki a ƙasa.
Majiyar jaridar Indaranka ta gano yadda al’umma da dama ke ci gaba da neman ɗaukin mahukunta kan halin matsin rayuwar da suka samu kan su a ciki, tun bayan da shugaban ƙasa Tinubu ya janye tallafin man fetur tun a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Yanzu haka dai mafi yawan gidajen man ƴan kasuwa a sassan jihar Kano, suna sayar da kowacce litar Fetur ɗaya akan kuɗi Naira 11,00, wasu kuma 1150, zuwa 1,200, yayin da na NNPCL ake sayarwa kowacce lita ɗaya 10,30, a Arewa maso Yammacin Najeriya, abin da ke damun al’umma.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
