Connect with us

News

Gobara Ta Kone Gidan Kakakin Majalisar Dokokin Zamfara 

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Wata gobara ta kone gidan kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Bilyaminu Moriki da ke Gusau.

Advertisement

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran majalisar, Bello Madaro ya fitar ranar Lahadi

Kungiyar Super Eagles Ta Yi Barazanar Kauracewa Wasan Da Za Ta Kara Da Kasar Libya

Madaro ya ruwaito magatakardan gidan, Mahmud Aliyu, yana bayyana bala’in a matsayin abin takaici.

Advertisement

Aliyu ya ce gobara ta lalata kadarori na miliyoyin Naira duk da cewa ba a yi asarar rayuka ba.

Ya ce, “Mahukuntan majalisar dokokin Zamfara sun kadu matuka kan gobarar da ta auku a ranar Lahadin da ta gabata da ta kone gidan kakakin majalisar da ke Gusau.

Advertisement

Madaro ya ce magatakardan na cewa, “A madadin ‘yan majalisar da daukacin ma’aikatan majalisar, ina jajantawa shugaban majalisar da iyalansa bisa wannan bala’i.”

Aliyu ya bukaci shugaban majalisar da iyalansa da su dauki lamarin a matsayin wani aiki na Ubangiji da ya kaddara.

Advertisement

Ya kuma roki Allah da ya kawar da sake aukuwar bala’in.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending