Connect with us

News

Ƴan Najeriya Na Kokawa Kan Rashin Kyawun Internet Da Saurin Ƙarewar Data

Published

on

wayoyin salula da na’urorin da ake shiga internet da su a Najeriya na kokaw

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Masu amfani da wayoyin salula da na’urorin da ake shiga yanar gizo da su a na kokawa kan rashin kyawun sadarwa da kuma saurin ƙarewar data a Najeriya.

Advertisement

Babu cikakken bayani kawo yanzu na musabbabin matsalar sadarwar da ake fuskanta a Najeriya.

Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’i sun sanar da tsunduma yajin aiki a faɗin Najeriya

To sai dai hakan na faruwa biyo bayan shugaban kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya Karl Toriola ya yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta ƙara kudin waya inda ya ce rashin yin haka zai kawo mummunar illa.

Advertisement

Ita ma hukumar sadarwa ta kasa NCC ta ga baiken kamfanin sadarwa na Starlink bisa ƙara kuɗin data ba tare da an amince masa ba, inda suka bayyana haka a matsayin karya dokokin hukumar.

NCC ta ce kamfanonin sadarwa dake amfani da tauraron ɗan adam sun ƙara kuɗin data.

Advertisement

Wane Masana kanan hakar yanar gizo ya ce datar da ake amfani da ita a yanzu tana karewa da wuri saboda a baya da babu manhajoji kamar TikTok da Youtube. Haka kuma akwai banbancin wayoyi domin na yanzu suna da saurin shanye data

Wannan dai na zuwa be daidai lokacin da Hukumar NCC, ta haramtawa ‘yan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 18 karbar layukan sadarwa da muka sani da Simcard.

Advertisement

Rahotanni daga hukumar na nuni cewa daukar wannan mataki na da nasaba da halin yanayin tsaro da kasar ke ciki yanzu haka da kuma baiwa iyaye damar sa ido da kuma siyan layukan da sunayensu a madadin ‘ya’yansu.

 

Advertisement

AFP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending