News
Yan Sanda Za Su Tono Gawar Wata Yarinya Mai Shekara Biyu Da Ake Zargin An Kashe
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta bayyyana cewa za ta tono gawar wata yarinya ‘yar shekara biyu da ta ke zargin an kashe tare da jefar da gawar ta a wani masallaci a karamar hukumar Ningi.
Kazalika, rundunar ta sanar da cewa ta kama mutane uku da ake zargin su na da hannu a kisan yarinyar, daga cikin su har da iyayen ta.
Gwamnan Kano Abba Kabir ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 Na N549,160,417,663.00
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, shi ne ya bayyana hakan yayin taron ganawa da manema labarai domin gabatar da masu laifin da rundunar ta kama.
WikkiTimes ta rawaito cewa rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa an samu gawar wata yarinya mai shekara biyu da aka jefar a wani masallaci a garin Niningi. Sai dai, ‘yan sanda sun ce babu wata alama da ke nuna cewa an yi wa yarinyar fyade.
SP Wakil ya bayyana cewa sun kama mahifin yarinyar, Abubakar Usman, mai shekara 23, da mahaifiyar ta, Lauratu Sale, mai shekara 17, da Kuma Aminu Adamu, wani mai shagon siyar da magani.
WikkiTimes ta samu labari daga majiya mai tushe cewa Abubakar da Lauratu sun haifi yarinyar ne ba tare da aure ba.
Lauratu ta bayyanawa ‘yan sanda cewa yarinyar ta kamu da ciwon zazzabi kuma ta kai ta wurin Aminu mai shagon magani an duba lafiyar ta amma kuma duk da haka ta rasu bayan sun dawo gida.
Bayan rasuwar yarinyar ne sai ta kira Abubakar tare da sanar da shi ya zo ya karbi gawar diyar sa domin ya je ya binne ta, amma sai ya ki zuwa saboda ba ya son asirin sa ya tonu.
Ganin haka ne ya sa Lauratu ta samu zani ta nade gawar yarinyar, wacce ta bawa dan uwan ta ya kai wa Abubakar.
Bayan Abubakar ya karbi gawar yarinyar ne sai ya faki idon mutane ya shiga masallaci ya ajiye ta, ya yi tafiyar sa.
Daga baya, Abubakar ya sanar da ‘yan sanda cewa bai yi wa gawar yarinyar komai ba, yadda ya karbi gawar a nade a zani, haka ya ajiye ta a Masallaci.
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa za ta tono gawar yarinyar ne domin sake gudanar da bincike a kan dalilin mutuwar ta tare da sanar da cewa za a gurfanar da wadanda aka kama da zarar an kammala bincike.
