News
Gwamnan Kano Abba Kabir ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 Na N549,160,417,663.00
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gabatarwa majalisar dokokin jihar sama da biliyan ɗari biyar da arba’in da tara, a matsayin ƙunshin kasafin kuɗin shekarar 2025.
BizPoint ta ruwaito cewa, kamar kasafin 2024, ilimi ya dauki kasu mai yawa a cikin kasafin 2025 tare da N168,350,802,346,19, wanda ke wakiltar kashi 31 na jimillar jimillar.
Wannan jarida ta tuna cewa ilimi ya samu kashi 29 cikin 100 na kasafin kudin shekarar 2024 na N437.3billion, amma ya dan samu sama da kasafin 2025 da aka gabatar
Da yake gabatar da kasafin gwamna Abba Kabir ya tabbatarwa da majalisar cewa wannan adadin kuɗin da aka ware da cewar za’ayi amfani da su ne wajen gudanar da ayyukan ci gaban rayuwar al’umma.
Abba Kabir ya kuma ce daga cikin ayyukan da za’a yi akwai inganta lafiyar al’umma da ilimi da samar da hanyoyi a faɗin jihar Kano, da dai sauran al’amuran more rayuwar al’umma.
“Saboda haka, cike da jin dadi da kuma kwarin guiwa na dora a gaban wannan majalisa mai girma, kasafin kudin 2025 na jihar Kano, wanda na yi wa lakabi da ”Budget of Bege, Capital Human and Economic Development,” Yusuf ya kammala.
