Connect with us

News

Gwamnoni Na Barazanar Hana Mu Takara A 2027 Matukar Muka Goyi Bayan Dokar Haraji Ta Shugaba Tinubu —Majalisar wakilai

Published

on

Majalisar wakilai ta ce gwamnonin na barazanar hana mambobinta takara a 2027 matukar suka goyi bayan dokar haraji ta Tinubu

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Majalisar wakilai ta ce gwamnoni na barazanar hana mambobinta takara a 2027 matukar suka goyi bayan dokar haraji ta  Shugaba Tinubu

Mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Mista Philip Agbese, ya bayyana cewa wasu gwamnonin jihohi suna barazanar hana ‘yan majalisar tarayya sake tsayawa takara a zaben 2027, matukar ba su janye goyon bayansu ga kudurin sauya fasalin haraji na Shugaba Bola Tinubu da ke gaban majalisar tarayya don tattaunawa ba.

Kungiyar Manyan Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aikin Gargadi A Najeriya 

Agbese ya kuma bayyana cewa ‘yan majalisar za su gana da Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Gyaran Haraji da Kudaden Shiga, Taiwo Oyedele, tare da wasu kwararrun masana haraji kan dokokin a yau Litinin.

Idan za a iya tunawa, a ranar 3 ga Satumba, 2024, Shugaban kasa ya tura daftarin kudirin gyaran dokoki hudu ga majalisar tarayya don tattaunawa, bayan shawarar kwamitin Oyedele.

Dokokin sun hada da Dokar Haraji ta Najeriya ta 2024, wadda ake sa ran zata sauya fasalin tattara haraji a kasar.

Advertisement

Sauran dokokin sun hada da ‘Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya’, wadda za ta soke dokar Hukumar Haraji ta tarayya (FIRS) tare da kafa Hukumar Haraji ta Najeriya.

Akwai kuma ‘Dokar Kafa Kotun Hadin Gwiwa Kan Haraji’, wadda za ta kafa kotun haraji da zata ringa bayarda hukunci kan dambarwar haraji idan ta taso.

Sai dai, gwamnonin jihohi 36 na kasar nan sun nemi a janye wadannan kudirori, suna masu ikirarin cewa akwai bukatar karin tattaunawa da kuma jin ra’ayoyin jama’a kafin yin doka akan sauye-sauyen.

Sai dai,Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi watsi da shawarar gwamnonin, yana jaddada cewa majalisar Dattijai da talwararta ta wakilai ne kadai ke da hakkin amincewa ko akasin haka ga kudirin dokokin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending