Connect with us

News

Abba Hikima Ya Maka Wike Da Wasu Mutane 5 A Kotu Tare da Neman Diyyar ₦500 Miliyan

Published

on

Abba Hikima Ya Maka Wike Da Wasu Mutane 5 A Kotu Tare da Neman Diyyar ₦500 Miliyan
lauya mai kare hakkin bil'adama, Abba Hikima

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wani lauya mai kare hakkin bil’adama, Abba Hikima, ya shigar da kara a kan Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda (IGP), da wasu mutane hudu a kan zargin take hakkin wasu masu rauni a Najeriya.

Advertisement

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa wadanda ake kara sun hada da Ministan Abuja, Nyesom Wike; Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda; Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS; Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC); da Antoni Janar na Tarayya.

Mutum 25 Sun Rasu Bayan Bullar Sabuwar Annoba Tare Da Kwantar Da Mutum 1, 160 A Sakkwato 

An shigar da karar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba, karkashin lamba FHC/ABJ/CS/1749/2024, bisa zargin rashin adalci da azabtarwa akan masu rauni, irin marasa matsuguni, ‘yan kasuwa kanana, da masu bara a Abuja.

Advertisement

Hikima, cikin karar da ya shigar, ya zargi wadanda ake kara da aikata abubuwan da suka saba wa Sashe na 34, 35, 41, da 42 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya (wanda aka gyara).

Ya bayyana cewa tsare mutane ba tare da wata shaida ba, cin zarafi, karbar kudi ta karfi, da kuma azabtarwa, wanda dukkansu ya saba wa kundin tsarin mulki kuma kuma hakan abun kunyata ne.

Advertisement

A karar da aka shigar karkashin Fundamental Rights (Enforcement Procedure) Rules 2009, Hikima yana neman abubuwa da dama. Wadannan sun hada da diyyar ₦500 miliyan a matsayin fansa ga mutanen da abin ya shafa da kuma neman afuwar jama’a .

Har ila yau, ya bukaci a gaggauta sakin wadanda aka tsare tare da mayar musu da kudaden da aka kwace daga gare su.

Advertisement

Sannan ya nemi a kawo sauye-sauyen manufofi don kare hakkin masu rauni a Najeriya, ciki har da wayar da kan jama’a kan hakkin bil’adama, tare da tilasta wa wadanda suke da alhakin take hakkin mutanen daukar nauyin abin da suka aikata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending