News
Kungiyar Miyatti Allah ta kirkiro taron shan fura da nono na Duniya
DAGA LAWAL ZUBAIRU
Akaron farku kungiyar Fulani ta miyyati Allah Koltol-Hore ta kasa ta kirkiro taron shan fura da nono na Duniya.
Taron da ya gudana ranar Juma’a 13/12/2024 a unguwar Tudun wada dake karamar hukumar Karu cikin jihar Nasarawa.
Shugaba Tinubu Da Manyan Yan Siyasa Sun Halarci Daurin Auren Ya’yan Sanata Barau Jibril Maliya
Kungiyar Fulani ta Miyyati Allah karkashin jagorancin Alhaji Bello Bodejo ta gudanar da taron bikin shan fura da Nonon shanu ta duniya tare da nuna al’adun Fulani.
Bayan bude kasuwar Shanu da bude sabon masallaci a Filin maliya aka cigaba da gudanar da taron shan Nono.
Taron da ya samu halartan manyan baki maza da mata da yan kasuwa daga sassa dabam dabam a arewacin Najeriya.
Da yake jawabin a madadin Alhaji Bello Bodejo Shugaban kungiyar na yankin Arewa ta gabas Injiniya Ibrahim Adamu.
Yace; wannan taro uku da aka hadasu waje daya karkashin jagorancin Alhaji Bello Bodejo. An gudanar da taron ne domin cigaban Arewa da qasa baki daya.
Yace; Alhaji Bello Bodejo ya Samar da wannan kasuwar ta sayar da dabbobi badan cigaban kansa ba. Sai dan cigaban Najeriya.
Yace; wannan kasuwar tana yankin Arewa ta tsakiya da ta hada bangarorin kasar baki daya.
Yace; yan kasuwa daga kowani sassa zasu iya haduwa domin hada hadan harkan kasuwanci a kasuwan maliya.
Yace; maliya itace babban kasuwan Dabbobi a kasan nan, a yanzu Wanda zata samar da cigaba mai tarin yawa.
Yace; kuma taron shan Nonon shanu yan nuna cigaban al’adun Fulani an kuma samar da Na’urar tatsan Nonon shanu da zasu iya shayar da al’umman Najeriya miliyoyin litan madara.
Ya kuma bayyana farin cikinsa da shirin Gwamnatin tarayya na kokarin Samar da ma’aikatan kiwon Dabbobi na qasa.
Shima a nasa jawabin Sanata Abdullahi Adamu, Wanda ya samu wakilcin Alhaji Shehu Tukur. Ya yabawa Bello Bodejo da kokarin da yayi na bunkasa kasuwar Dabbobi a wannan yankin ta Arewa.
Yace; Bello Bodejo mutumne da yayi abin bajinta Dan cigaban harkan tattalin arziki a kasa .
Alhaji Shehu Tukur yayi kira ga yan kabilar Fulani dasu zama masu hadin kai da tabbatar da zaman lafiya.
Yace; Allah ya azuta Fulanin Najeriya da arzikin Shanu. Dan haka su zauna lafiya da kowata kabila.
Daga karshe anyi adu’ar Allah ya kwato Shugaban kunhiyar Alhaji Bello Bodejo daga tsare shi da akayi a hannun jami’an tsaro.
