Connect with us

News

Shugaba Tinubu  Da Manyan Yan Siyasa Sun Halarci Daurin Auren Ya’yan Sanata Barau Jibril Maliya  

Published

on

FB IMG 1734115713888
  1. DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

A yau Juma’a aka gudanar da daura Auren Ya’yan mataimakin shugaban majalisssar dattatwan Sanata Barau Jibril Maliya  Yar gidan Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero da Dan Gidan Abdulmunaf Sarina.

 

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas da  Gwamnoni da dama da Sanatoci ne suka Halarci taran daurin Auren.

Haka zalika Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da dan gidan tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari Yusuf Buhari da  Mamman Daura suma suna daga cikin manyan baki a wajen daurin Auren.

Advertisement

 

Jaridar Inda ranka ta rawaito cewa  dan Sanata Barau, Jibrin  Abba Barau  shine ya  auri Maryam Nasir Ado Bayero, Yar  Sarkin Bichi sai kuma Aisha Barau Jibrin wanda aka daura auren ta da  Injiniya Abubakar, Da’.ga Dr Abdulmunaf Yunusa Sarina, shugaban rukunin kamfanonin Azman.

Advertisement

Rahotanni sun tabbar da cewa shugaba Tinubu ne  ya zamto a matsayin Wakili da Waliyyi ga ‘ya’yan mataimakin shugaban majalisar dattawa ta bakin  kakakin majalisar wakilai tajuddin Abbas.

 

Advertisement

A yayin da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa Dr  Abdullahi Ganduje ya kasance Waliyyi  ga diyar Sarkin Bichi, a yayin da tsohon  Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Tanko Almakura, ya kasance Wakili na Abubakar, dan Dakta Abdulmunaf Sarina Wanda   Limamin masallaci na  kasa Farfesa Ibrahim Maqari  ya jagoranta.

 

Advertisement

 

Cikin manyan bakin da suka halarci daurin Auren sun hadar da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq da  Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah; Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda.

Advertisement

 

Sai kuma hwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni da dai sauransu manyan baki daga gida da wajen Nageriya.

Advertisement

 

Cikin Sanatocin da suka halarci taron Auren  sune shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da  Ali Ndume da Sani Musa, Ibrahim Mohammed Boma da  Aminu Iya Abbas da  Buhari Abdulfatai da Mohammed Tahir Monguno da  Ikira Aliyu Bilbis da  Mohammed Ogoshi Onawo da  Salihu Mustapha da Shehu Buba da  Abdul Ningi da  Abdullahi Yahaya da Ahmed Lawan da Sahabi Ya’u da  Kamorudeen Adekunle Adedibu, Danjuma Goje.da Lawal Usman da  Kawu Sumaila.

Advertisement

 

 

Advertisement

Wakilan majalisar ECOWAS duk sun halarci taron  da mataimakin shugaban majalisar na hudu, Billay G Tunkara.

Mataimakan shugaban kasa da suka hada da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, shugaban ma’aikata, tsohon kakakin majalisar wakilai, Rt Hon Femi Gbajabiamila, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, mataimaki na musamman kan harkokin tsaro. Shugaban (Al’amuran Siyasa), Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa Kan harkokin yada labarai  Abdulaziz Abdulaziz, duk sun halarci taron

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending