News
Gwamnan Kano Ya Kori Baffa Bichi Da Sagagi Da Wasu Kwamishinoni Guda 5
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf, ya sanar da sake fasalin majalisar zartarwa ta jihar domin tabbatar da daidaituwar harkokin siyasa a gwamnatinsa.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan babban canji na farko a majalisar zartarwarsa ya fara aiki nan take.
DA DUMI-DUMI : Gwamna Abba Kabir Ya Kori Wasu Daga Cikin Kwamishinan Sa
Daga cikin wadanda canjin ya shafa sun hada da Shugaban Ma’aikata, Alh. Shehu Wada Sagagi, wanda aka soke ofishinsa, da kuma Sakataren Gwamnatin Jiha, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, wanda aka cire saboda matsalolin lafiya.
A cewar Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Gwamna Yusuf ya sauke wasu mambobin majalisar zartarwa sannan ya mayar da wasu zuwa wuraren da za su inganta aikin mulki jihar.
Daga cikin wadanda suka ci gaba da rike mukamansu akwai:
Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a, Bar. Haruna Isa Dederi,
Kwamishinan Noma, Dr. Danjuma Mahmoud,
Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran,
Kwamishinan Filaye da Tsare-tsare, Hon. Abduljabbar Mohammed Umar,
Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Hon. Musa Suleiman Shannon,
Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, Injiniya Marwan Ahmad.
Haka zalika, wadanda suka ci gaba da rike mukamansu sun hada da:
Kwamishinan Albarkatun Ma’adanai, Sefiyanu Hamza,
Kwamishinan Harkokin Addini, Sheikh Ahmad Tijjani Auwal,
Kwamishinan Matasa da Wasanni, Hon. Mustapha Rabiu Kwankwaso,
Kwamishinan Zuba Jari da Kasuwanci, Adamu Aliyu Kibiya,
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Sabis na Musamman, Manjo Janar Mohammad Inuwa Idris (mai ritaya).
An mayar da wasu zuwa sabbin ma’aikatun da suka hada da:
Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdulssalam, daga Ma’aikatar Kananan Hukumomi zuwa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi,
Hon. Mohammad Tajo Usman daga Kimiyya da Fasaha zuwa Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta,
Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata daga Ilimi Mai Zurfi zuwa Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire.
Sauran sun hada da:
Hon. Amina Abdullahi daga Jin Kai da Rage Talauci zuwa Ma’aikatar Mata, Yara da Nakasa,
Hon. Nasiru Sule Garo daga Muhalli da Sauyin Yanayi zuwa Ma’aikatar Ayyuka na Musamman,
Hon. Ibrahim Namadi daga Kulawa da Ayyuka zuwa Ma’aikatar Sufuri,
Hon. Umar Haruna Doguwa daga Ilimi zuwa Ma’aikatar Albarkatun Ruwa,
Hon. Ali Haruna Makoda daga Albarkatun Ruwa zuwa Ilimi,
Hon. Aisha Lawal Saji daga Ma’aikatar Mata, Yara da Nakasa zuwa Al’adu da Yawon Bude Ido,
Hon. Muhammad Diggol daga Sufuri zuwa Kulawa da Ayyuka.
A gefe guda, Gwamnan ya sauke kwamishinoni guda biyar daga majalisar zartarwa da suka hada da:
Ibrahim Jibril Fagge, Ma’aikatar Kudi,
Ladidi Ibrahim Garko, Al’adu da Yawon Bude Ido,
Baba Halilu Dantiye, Bayani da Harkokin Cikin Gida,
Shehu Aliyu Yammedi, Ayyuka na Musamman,
Abbas Sani Abbas, Raya Karkara da Ci Gaban Al’umma.
Haka kuma, Gwamnan ya umarci Shugaban Ma’aikata da sauran kwamishinonin da akacire su kai kansu ofishin Gwamna domin yiwuwar sake ba su wasu ayyuka.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
