News
Naira Miliyan 1.2 Kawai Masu Sana’ar POS Za Su Iya Amfani Dasu A Kowacce Rana – CBN
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babban bankin Najeriya CBN ya taƙaita hada-hadar kuɗin ga masu Sana’ar PoS zawa naira miliyan 1200,000 a kowacce rana.
Wannan umarnin na ƙunshi ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Talata game da taƙaita hada-hadar kuɗi ga wakilan bankuna.
“Bankin ya ɗauki wannan matakin ne domin ƙara jawo hankalin masu hada-hadar kuɗi zuwa ga rage amfani da tsabar kuɗi,” kamar yadda sanarwar, wadda Oladimeji Yisa Taiwo ya sa hannu a madadin daraktan tsare-tsaren fitar da kuɗi.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa kwastoma ba zai cire sama da naira 500,000 ba a mako.
Advertisements
