Connect with us

News

Ba’Bu Wata Gaskiya A Mulkin Shugaba Tinubu Da Buhari — Sule Lamido

Published

on

Sule Lamido

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce shugaba Bola Tinubu da tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari basa kwatanta gaskiya wajen gudanar da mulkinsu.

Sule Lamido ya zargin ‘wadannan Shugabannin Biyu da suka fito daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC ya ce sam’sam ba su da gaskiya a harkokin mulkinsu.

Advertisement

Sule Lamido wanda ya bayyana hakan cikin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, ya ce salon mulkin jam’iyyar APC ya sha bamban da yadda ake gudanar da mulkin jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP Wanda , take bayyanawa Yan Nageriya tsantasar gaskiya a wajen gudanar da mulkinta.

Ya ce: “Gwamnatin Buhari da Tinubu ba sa nuna gaskiya ga ‘yan Najeriya, sabanin lokacin da PDP ke mulki, inda komai ya kasance a bayyane kuma a bude ga dukkan ‘yan Najeriya a cewarsa.

Advertisement

“Amma da zuwan Buhari, ya fara yaudara kuma rashin gaskiya suka tabbata a tafiyar da gwamnatisa.

Yayin da yake kokawa kan dimbin bashin da ake bin kasar, Mista Lamido ya koka da cewa Abin da gwamnati ke gaya wa ‘yan Najeriya ya bambanta da abin da take aiwatarwa.

Advertisement

Idan ana gaya wa ‘yan Najeriya gaskiya to babu laifi a cikin hakan, amma ta yaya za ku yi kasafin Naira Tiriliyan 30 kuma a samar da Naira Tiriliyan 50 , wanda harda bashi a ciki lamuni.a ciki tom yaya za’ayi da rarar Tiriliyan 20.

Ya kuma kara da cewa, “wannan sakaci da nuna son kai ba a ko’ina a duniya ake yi ba, amma duk da haka sai ka ga wasu‘yan Najeriya suna goyon bayansa. Ku ziyarci shafukan sada zumunta, ku ga yadda ake sukar APC, ana kiran su da bala’i, amma sai ka ga wasu suna kare gwamnati

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending