News
2025 :Baza Mu Dauki Halin Kunnen Uwar Shegu Da Gwamnati Ke Yiwa Muradin Su Ba —Kungiyar ASUU
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi gargadin cewa shekarar 2025 za ta kasance shekarar da baza su dauki halin kunnen uwar shegu da gwamnati ke yiwa muradin su ba .
A cewar kungiyar kokarin da gwamnatin tarayya ta yi na magance matsalolinta a shekarar 2024, kawai shashi fadi ne babu wani abunda ta aiwatar .
Na’ Bar Tafiyar Buhari Ne Sabida Ya Cutar Da Yan Najeriya Musanman Ma Talakawa – Rarara
Haka kuma Kungiyar ta soki yadda gwamnati ta yi watsi da tsarin jami’o’i da kuma gazawarta wajen warware matsalolin jami’o’i har yanzu.
A nasa jawabin Farfesa Ayo Akinwole, Shugaban ASUU reshen Ibadan, ya bayyana cewa hakuri da kungiyar tayi a shekarar da ta wuce bata katse karatu ta tafi yajin aiki ba sadaukarwa ne ba wai dan gwamnatin ta yi wani hobbasa ba.
Haka kuma Kungiyar ta ASUU ta yi Allah-wadai da irin yadda gwamnatin ta sauya tsarin shiga jami’a a shekaru 18, Ta kuma nemi gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da ta sake duba daftarin yarjejeniyar da Nimi Briggs ya jagoranta
