Connect with us

News

DA DUMI-DUMI:  Kwamishina Ya Yi Murabus A Kano

Published

on

DAGA YADIR SANI  ABDULLAHI 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da ajiye aiki da Engr. Muhammad Diggol, yayi a matsayinsa na kwamishinan ma’aikatar bibiyar aiyuka nan take.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Jaridar INDA RANKA a ranar Lahadi.

Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, Ya Taya Gwamna Yusuf Murnar Cika Shekaru 62, Ya Bayyana Shi A Matsayin Shugaba Mai Hange

Tun a farkon mulkinsa gwama Abba Kabir Yusuf ya nada Engr. Muhammad Diggol a matsayin kwamishinan sufuri, kafin daga bisani ya saura masa wajen aiki zuwa ma’aikatar bibiyar aiyuka inda a nan ne yayi murabus .

Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa ga Engr. Diggol bisa kokarinsa da jajircewarsa, sadaukarwa, da kuma bin ka’idojin aiki a lokacin da yake zama dan majalisar zartarwa ta jiha.

A cewar sanarwar, Gwamnan ya yiwa Engr. Doggol fatan alheri a harkokin da zai sanya a gaba.

Advertisement

Sanarwar dai ba ta bayyana dalilin da ya sanya kwamishinan ya ajiye aikinsa ba.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending