News
Hukumar EFCC Ta Kori Jami’anta 27 Bisa Laifin Zamba Da Rashin Da’a
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci A Najariya ta kori jami’anta 27 bisa laifin zamba da rashin da’a
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar ranar Litinin a birnin Abuja.
Abba @62: Kanawa Suna Da Shugaba Mai Hangen Nesa Da Tausayin Al’ummar Jihar —Dr. Labaran
Oyewale ya bayyana cewa ma’aikatan an kore su ne saboda aikata laifuka daban-daban da suka shafi zamba da rashin da’a.
Sai dai, hukumar ba ta bayyana sunayen waɗanda aka sallama ba.
A cewarsa, sallamar su ta biyo bayan shawarar Kwamitin Ladabtar da Ma’aikata na EFCC tare da amincewar Shugaban Hukumar, Ola Olukoyede.
Advertisements
