Connect with us

News

Abba @62: Kanawa Suna Da Shugaba Mai Hangen Nesa Da Tausayin Al’ummar Jihar —Dr. Labaran

Published

on

DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Shekarun Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano an bayyana su a matsayin albarka ga al’ummar jihar.

Advertisement

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da sashen hulda da jama’a na ma’aikatar ya fitar, kuma aka rarraba wa manema labarai.

Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Yar Sakataren Gwamnatin Sokoto Da Jikokin Sa 

Dr. Labaran ya yi wannan jawabi ne cikin farin ciki da murnar zagayowar ranar haihuwar Alhaji Abba Kabir Yusuf karo na 62.

Advertisement

Ya bayyana cewa, irin yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke canza Kano zuwa babbar birni tare da mayar da hankali kan tsarin kiwon lafiya ya nuna cewa al’ummar Kano suna da shugaba mai hangen nesa da tausayin al, ummar jihar .

Kwamishinan ya tunatar da jama’a cewa tun lokacin gwaman Kano yake kwamishinan ayyuka a lokacin mulkin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, His Excellency ya nuna kaunarsa ga jihar ta hanyar gudanar da ayyuka da dama da suka sauya fuskar Kano.

Advertisement

Dr. Labaran ya bayyana cewa tun bayan da wannan gwamnati ta kama aiki, Alhaji Abba Kabir Yusuf bai bari barazanar cikin gida ko ta waje su hana shi cimma manufofin sa na samar da jagoranci mai ma’ana ba.

Ya ce, “Abin lura ne cewa Gwamna Abba Kabir yana bayar da jagoranci mai nagarta wanda ya sauya tsarin siyasar jihar

Advertisement

“Aikin gwamnan yana gudana cikin awa 24 na kowace rana; yana zagayawa dare da rana don sa ido kan ayyuka, asibitoci, da sauransu don ganin komai da kansa. Lallai, shekarun Alhaji Abba Kabir Yusuf albarka ne ga dukkanmu.”

Ya taya al’ummar jihar murna bisa samun shugaba mai hangen nesa, jajircewa, da tausayi, wanda yake aiki tukuru don ganin an kyautata jihar tare da inganta walwalar rayuwar al’umma. Ya kuma yi kira ga mutane da su ci gaba da marawa manufofinsa na ci gaban al’umma baya domin inganta jihar Kano.

Advertisement

A ƙarshe, Dr. Labaran ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da ba da jagoranci da kariya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ci gaba da bayar da jagoranci mai ma’ana dakowa ke so.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending