Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Wani Masallaci A Zamfara, Sun Sace Daruruwan Masu Ibada

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Rahotanni na nuni da cewa wasu masu garkuwa da Mutane sun kai hari kan wani masallaci a kauyen Birnin Yaro, jihar Zamfara, inda suka sace masu ibada da dama.

A cewar Zagazola Makama, dan jaridar dake mayar da hankali kan yaki da ‘yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi, ya ce Bello Turji tare da mutanensa ne suka jagoranci harin yayin sallar Isha a daren Juma’a.

Sojojin Nijeriya sun tarwatsa sansanin Bello Turji, sun kashe ‘yan ta’adda 25 a Zamfara

Masu harin sun tasa wadanda suka sace zuwa cikin daji, kuma ba a san yawan mutanen da aka sace ba har yanzu.

Wata majiya ta ce Turji na iya amfani da mutanen a matsayin garkuwa don kare kansa daga harin dakarun sojin Najeriya na Operation FANSAN YANMMA kan maboyarsa.

A ‘yan kwanakin nan, sace-sacen mutane don kudin fansa ya karu sosai a arewacin Najeriya.

Advertisement

A makon da ya gabata, akalla mutane 46, ciki har da mata da yara, an sace su a wani hari da aka kai Gana, wani gari a jihar Zamfara.

A watan Disamba, akalla mutane 43 aka sace a Kakidawa, Gidan Goga, karamar hukumar Maradun ta jihar.

Shaidu sun bayyana cewa masu garkuwa sun yi harbe-harbe ba kakkautawa, wanda ya sa mazauna garin suka tsere zuwa cikin daji.

Sun kuma ce masu garkuwar sun yi bincike daga gida zuwa gida, inda suka sace mata da yara da suka kasatserewa.

 

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending