News
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Kafa Sabuwar Kwalejin Kimiyya Da Fasaha A Abuja Tare Da Sanya Mata Sunansa A Abuja
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa Kwalejin Kimiyya ta tarayya a yankin Gwarinpa na babban birnin tarayya (FCT), wadda za ta kasance a matsayin “Kwalejin Kimiyya Ta Bola Ahmed Tinubu, Gwarinpa.” An kafa ta don tallafawa ilimin fasaha, da sana’o’i, da kuma kasuwanci a Nijeriya.
A cikin wata wasiƙa da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya aika wa Ministan FCT, Nyesom Wike, a ranar 16 ga Janairu, 2025, ya nemi a ware wurare da suka dace don kafa rukunin wucin gadi da na dindindin na makarantar. Kwamitin fasaha daga ma’aikatar ilimi da hukumar NBTE za su duba wuraren kafin ba da izinin ƙarshe.
Tankar Mai Ta Kuma Faduwa A Niger Inda Mutane Sunje Ɗiban Ganima.
Shugaban ƙaramar hukumar AMAC, Christopher Zakka Maikalangu, ya yabawa shugaban ƙasa bisa wannan matakin, yana mai cewa kafa makarantar zai ƙara wa mazauna FCT ci gaba da ilimi mai amfani.
