News
Ma’aji Ya Nuna Bacin Rai Kan Aikin Makaranta a Doguwa, Ya Bada Sammacin Dan Kwangilar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Yadda Ake Ba da Kwangiloli da Bibiyar Ayyukan Gwamnatin Jihar Kano, Kwamared Nura Ma’aji Sumaila, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda aka kasa samun ci gaba a aikin ginin Kwankwasiyya Gida-Gida na ajujuwa hudu (4) a garin Rufa’i, karamar hukumar Doguwa.
A ranar Alhamis, yayin rangadin sa ido, Kwamishinan ya nuna damuwarsa kan yadda dan kwangilar ya gaza fitowa fili duk da kaso na kudin da aka riga aka biya.
An Dakatar Da Sheikh Bin Uthman Daga Limancin Masallacin Sahaba, DSS Ta gayyace shi
Ya bayyana cewa, tun bayan ziyarar sa ido da ake yi, ya gamsu da yawancin ayyukan da ya ziyarta, sai dai abin da ya gani a garin Rufa’i bai masa dadi ba.
> “Wannan shi ne kawai aikin da ke ba mu ciwon kai tare da dan kwangilar,” in ji shi.
> “Na ba da umarnin a kira dan kwangilar, ya zo ofishin gobe domin mu ji ta bakinsa kai tsaye.”
Kwamared Ma’aji ya jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci sake-saken aiki ba, domin an kuduri aniyar aiwatar da ayyuka masu inganci. Ya nanata cewa za a ci gaba da kare muradun al’umma tare da tabbatar da gaskiya, rikon amana, da kimar kudi wajen aiwatar da ayyukan gwamnati a fadin jihar Kano.
A yayin rangadinsa, Kwamishinan ya duba ayyuka guda shida a kananan hukumomin Kiru, Tudun Wada, da Doguwa, wanda suka hada da:
Aikin inganta cibiyar lafiya daga Kafin Mai Yaki zuwa babban asibiti.
Aikin titin Tudun Wada mai tsawon kilomita 5.
Gyaran gaba daya na Kwalejin Fasaha da Kimiyya Rabiu Musa Kwankwaso a Tudun Wada.
Ginin titin kilomita 5 a karamar hukumar Doguwa.
Ginin Kwankwasiyya Gida-Gida na ajujuwa hudu (4) a Model Tudun Wada da garin Rufa’i.
Kwamishinan ya nanata cewa za a dauki matakin da ya dace kan duk wani dan kwangila da ya gaza cika alkawuran da aka yi masa, domin ci gaban jihar da kuma inganta rayuwar al’umma.
