Connect with us

News

APC Ta Sanar Da Dalilan Korar Tsohon Gwamnan Jihar Osun Rauf Aregbesola Daga Jam’iyyar  

Published

on

1738506387278

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

A makon da mukayi bankwana dashi Jam’iyyar APC ta ta kori tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon ministan cikin gida Rauf Aregbesola daga cikinta bisa zarginsa da yiwa Jam’iyyar zagon Kasa.

 

Advertisement

Tun da fari jam’iyyar ta zargi Aregbesola da aikata wasu abubuwa da suka saba wa jam’iyyar da kuma wasu abubuwa dake kama da makarkashiya domin kifar da jama’iyyar.

 

Advertisement

Cikin wata sanarwar da jam’iyyar ta fitar ta tabbatar da korar Rauf Aregbesola

 

Advertisement

Aregbesola, wanda ya kasance ministan cikin gida a lokacin gwamnatin da ta gabata wanda ya jagoranci wani bangare na jam’iyyar  a jihar a bangaren da aka yi wa lakabi da “The Osun Progressives,” wanda kuma daga baya aka sake masa lakabi da ”Omoluabi Caucus”.

 

Advertisement

Korar tsohon gwamnan ta biyo bayan taron da bangaren da yake jagoranta wato Omoluabi Caucus, ya gudanar kuma karkashin jagorancin, Aregbesola.

 

Advertisement

A lokacin taron bangaren ya sanar da aniyarsa ta ficewa daga APC,inda ya bayar da hujjar rashin tasirin jam’iyyar a jihar kwata-kwata.

 

Advertisement

Sai dai kuma tun kafin ya tabbatar da haka ga magoya bayansa jam’iyyar APC ta sanar da korarsa daga jam’iyyar.

 

Advertisement

Aregbesola wanda yana ɗaya daga cikin makusantan shugaban Kasa Bola Tinubu a wancan lokacin sun raba jiha ne tun bayan kokarin maida tsohon gwamnan jihar Gboyega karo na biyu a zaben gwamnan jihar.

 

Advertisement

Aregbesola ya ja layi tsakaninsa da Tinubu inda hatta a zaɓen sa na shugaban kasa, bai goywa Shugaba Tinubu baya ba.

Sai dai Kuma wasu na ganin cewa ba garamin gibi Jam’iyyar APC zata samuba Musamman ma irin magoya bayan da yake dasu.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending