Connect with us

News

NDLEA Ta Kama Dattijo Mai Shekaru 75 da Zargin Siyar da Kayan Maye ga Matasa

Published

on

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jami’in Hukumar NDLEA

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta cafke wani dattijo mai shekaru 75 mai suna Baba Nuhu, da ake zargi da siyar da kayan maye ga matasa a kauyen Tumbau, karamar hukumar Gezawa.

Advertisement

Mai magana da yawun hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya bayyana wa PM NEWS cewa Baba Nuhu ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, yana mai ikirarin cewa wannan sana’a ce da ya dogara da ita tsawon shekaru biyu.

Jami’an Hukumar EFCC Sun Gurfanar Da Manajan Darakta Kan Damfarar Kudade A Gombe

A cewar Maigatari, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi ba ta tsaya ga matasa kadai ba, har da manyan mutane.

Advertisement

Daga cikin haramtattun kwayoyin da aka samu a hannun wanda ake zargi sun hada da Tramadol, Diazepam, Exol da wasu miyagun kwayoyi masu hadari.

Hukumar NDLEA ta tabbatar da cewa za a gurfanar da Baba Nuhu a gaban shari’a domin ya fuskanci hukunci bisa doka. Haka kuma, hukumar ta yi kira ga jama’a da su guji saye ko sayar da kayan maye, tare da bayar da hadin kai wajen kawar da wannan annoba daga cikin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending