News
Dattijo Mai Shekaru 50 Ya Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga, Sun Yi Garkuwa Da Ɗansa Da Iyalansa
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
An kama wani dattijo mai shekaru 50, Ado Haruna, bisa laifin ba da bayanan sirri ga ‘yan bindiga, inda suka yi garkuwa da ɗan yayarsa, Alhaji Bashiru Anas, tare da iyalansa a Zariya, Jihar Kaduna.
Duk da cewa an biya har Naira miliyan 13 a matsayin kudin fansa, tare da sabbin babura hudu da katin kiran waya na Airtel na Naira 300,000, Haruna ya samu Naira 200,000 kacal daga rabon kudin.
Ribadu Ya Nemi Naja’atu Ta Janye Kalaman Zargi Kansa Ko Su Wanye A Kotu
Jami’an rundunar lalubo bayanan sirri sun cafke Haruna, wanda aka bayyana a Abuja a matsayin daya daga cikin mutanen da ke da hannu a manyan laifuka.
Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, ya jagoranci wasu ‘yan bindiga uku zuwa gidan Alhaji Anas da tsakar dare, inda suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa bayan sun tarar da shi ba ya nan.
An tsare iyalin har tsawon kwanaki 60 a dazukan Buruku da Sabo Birni. A lokacin da yake tabbatar da rawar da ya taka, Dattijo mai shekaru 50 ya amsa cewa ya nuna wa ‘yan bindiga gidan Alhaji Anas, wanda ya kira da “dan yayata.”
Wannan kame na kara tabbatar da yadda wasu ke hadin baki da ‘yan ta’adda don cutar da na kusa da su, duk da irin radadin da hakan ke haifarwa ga iyalai da al’umma baki ɗaya.
