Connect with us

News

KASO 95% Na Kungiyoyin Fararen Hula a Kano Sun Goyi Bayan Matakin Gwamnatin Jihar na Tantance Ayyukansu

Published

on

IMG 20250224 WA0006

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula a Kano (KCSF) ta bayyana goyon bayanta ga matakin Gwamnatin Jihar Kano na kafa kwamitin tantance ayyukan kungiyoyin farar hula, domin inganta ayyuka da kare mutuncin jihar.

Advertisement

A cikin taron manema labarai da kungiyar ta KCSF ta gudanar, wanda ya samu halartar kungiyoyi 87 karkashin jagorancin Kwamarred Salisu Gambo Ditol, an bayyana matakin gwamnatin a matsayin wani babban ci gaba wajen tabbatar da ingantattun ayyuka da gujewa matsalolin da ke tasowa daga kungiyoyin da ba su da tsari.

KCSF Ta Yi Maraba Da Matakin Gwamnatin Kano Na Kafa Kwamitin Tantance Ayyukan Kungiyoyin Farar Hula

KCSF ta jaddada cewa wannan tantancewa zai taimaka wajen dakile ayyukan da ke saba wa al’ada da dokokin kasa, musamman ma wadanda ke tallafawa dabi’u marasa kyau kamar auren jinsi (LGBT) da wasu kungiyoyin da ake zargin suna daukar nauyin ta’addanci.

Advertisement

A cewar gamayyar, “Mun yi imanin cewa kafa wannan kwamitin tantance ayyuka wata dama ce ta tabbatar da gaskiya da inganci a cikin ayyukan kungiyoyin farar hula. Wannan zai taimaka wajen kawar da duk wata matsala da ka iya kawo tarnaki ga ci gaban al’umma.”

Kungiyar ta bukaci a gudanar da aikin tantancewar cikin gaskiya da adalci tare da bai wa kowacce kungiya damar bayyana kanta da nagartar ayyukanta.

Advertisement

A karshe, KCSF ta bayyana shirinta na baiwa kwamitin goyon baya domin ganin an cimma burin da ake bukata wajen inganta ayyukan kungiyoyin farar hula a jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending