Connect with us

News

KCSF Ta Yi Maraba Da Matakin Gwamnatin Kano Na Kafa Kwamitin Tantance Ayyukan Kungiyoyin Farar Hula

Published

on

IMG 20250224 WA0006

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula ta Kano (Kano Civil Society Forum – KCSF), wadda ke karkashin jagorancin kungiyoyi 87 na matasa, ta bayyana goyon bayanta ga matakin Gwamnatin Jihar Kano na kafa kwamitin tantance ayyukan kungiyoyin masu zaman kansu, domin tabbatar da ingantattun ayyuka da gujewa duk wata matsala da ka iya tasowa daga ayyukan da ba su da tsari.

KCSF ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da cewa dukkan kungiyoyin masu zaman kansu suna bin ka’idojin aiki da dokokin kasa, tare da tabbatar da ingantaccen gudunmawa ga cigaban al’umma.

Gidauniyar Attahiru Bafarawa Ta Bada Tallafin Karatu na Shekara Uku ga Dalibai 108 a Jihar Sokoto

A cewar gamayyar, “Mun yi imanin cewa kafa wannan kwamitin tantance ayyuka wata dama ce ta tabbatar da gaskiya da inganci a cikin ayyukan kungiyoyin farar hula.

Wannan zai taimaka wajen kawar da duk wata matsala da ka iya kawo tarnaki ga ci gaban al’umma.”

KCSF ta jaddada bukatar hadin kai tsakanin Gwamnati da kungiyoyin farar hula wajen aiwatar da aikin tantancewar cikin gaskiya da adalci. Hakanan ta bukaci a baiwa kowacce kungiya damar bayyana kanta tare da nuna nagartar ayyukanta.

Advertisement

Gamayyar ta kuma bayyana shirinta na baiwa kwamitin goyon baya domin ganin an cimma nasarar da ake bukata.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending