Connect with us

News

Yadda Cacar-baka Ta Ɓarke Tsakanin Trump Da Zelensky A Fadar White House

Published

on

Yadda cacar baka ta ɓarke tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky a fadar White House

 

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soke taron manema labarai da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, bayan wata ganawa da ta rikide zuwa cacar baki a bainar jama’a a ranar Juma’a.

Advertisement

Zelenskyy na ziyarar aiki a Amurka don tattauna yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Ukraine da Rasha da kuma neman karin tallafin soji daga sabuwar gwamnatin Amurka.

DA DUMI-DUMI: An Tabbatar Da Ganin Watan Ramadan A Naeriya, Azumi Zai Fara Gobe

Sai dai ganawar da aka yi da safiyar Juma’a a Ofishin Oval ta kasance mai zafi, inda Trump, Zelenskyy da Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance suka yi musayar kalamai kai tsaye a gaban ‘yan jarida kan bambancin ra’ayinsu dangane da halin da Ukraine ke ciki.

Advertisement

Bayan ganawar, Trump ya soke taron manema labarai da aka shirya yi da Zelenskyy, yana mai zargin shugaban Ukraine da nuna rashin girmamawa ga Amurka.

“Ya nuna rashin girmamawa ga Amurka a cikin Ofishin Oval mai daraja,” in ji Trump a shafinsa na Truth Social. “Zai iya dawowa idan ya shirya don zaman lafiya.”

Advertisement

Wannan lamari na kara dagula dangantakar diflomasiyya tsakanin sabuwar gwamnatin Trump da Ukraine, yayin da yakin Ukraine da Rasha ke ci gaba da barazana ga tsaron duniya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending