News
Abia, Kano da Ebonyi Sune Kan Gaba Wajen Yawan Yaran da Ba Sa Kammala Babbar Sakandare – Rahoto
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A wani sabon bincike da aka gudanar, jihohin Abia, Kano da Ebonyi sun fi yawan yaran da ba sa kammala karatun babbar sakandare (SSS) a Najeriya. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta ke ci gaba da zama barazana ga cigaban ilimi a ƙasar.
Rahoton da Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Kasa (NSSEC) ta fitar na zangon karatu na 2023/2024 ya nuna cewa kimanin ɗalibai 127,067 ne suka daina zuwa makaranta a jihohi 20 daga cikin 36 da ake da su a Najeriya.
An Kama Wasu ‘Yan Pakistan Biyu Kan Jagorantar Kungiyar Masu Garkuwa Da Mutane A Legas
Jihar Abia ce ke kan gaba da ɗalibai 36,700 da ba sa zuwa makaranta, inda kaso 56.43% daga cikinsu maza ne. Yawancin waɗannan yara suna barin makaranta ne a matakin SS1 da SS2, a yayin da suke shirin shiga matakin karshe na makaranta.
A jihar Kano kuwa, adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya kai 30,863, inda yawancin su mata ne. Rahoton ya bayyana cewa matsalolin talauci, auren wuri da bambance-bambancen al’ada na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara cigaba da karatu.
Jihar Ebonyi na da yara 13,048 da ba sa zuwa makaranta, wanda hakan ke nuna cewa yankin kudu maso gabas ba ya baya a wannan matsala.
Dalilan da Ke Hana Yara Kammala Makaranta
Masana sun danganta wannan matsala da:
Talauci
Matsalar tsaro
Auren wuri
Rashin ingantaccen tsarin tallafi
Sauya wurin zama
HANYOYIN MAGANCE MATSALAR
Shugabar wata makaranta a Kano, Hajiya Maryam Magaji, ta ce dole ne a haɗa hannu tsakanin gwamnati, makarantu masu zaman kansu da shugabannin al’umma don magance wannan matsala.
“Bai kamata a bar batun ilimi a hannun gwamnati kawai ba, dole a samu hadin gwiwar al’umma domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta,” in ji ta.
Matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na ci gaba da zama babban ƙalubale ga cigaban Najeriya. Masana na ganin cewa sai an mayar da hankali kan tallafin karatu, wayar da kai da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma, sannan za a iya rage yawan yaran da ke daina zuwa makaranta.
