Connect with us

News

Yayin da Duniya Ke Karrama Ranar Mata: Ina Aka Kwana a Batun Kare Hakkokinsu?

Published

on

download

 

Kare hakkin mata, samar da daidaito mai dorewa, da kuma tabbatar da hanyoyin dogaro da kai wa mata da ‘yan mata a duniya baki ɗaya shi ne taken bikin Ranar Mata ta Duniya na 2025. Wannan rana ta musamman na zuwa ne daura da cika shekaru 30 da rattaba hannu kan yarjejeniyar Beijing, wadda ta zama ginshikin sauye-sauyen da suka inganta rayuwar mata a duniya.

A shekarar 1995, Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da babban taro na hudu kan batun mata, inda kasashe 183 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta ƙunshi matakan inganta rayuwar mata ta fannoni daban-daban.

Gwamnatin Kano Ta Bankaɗo Mutane 8,875 Da Ke Zuƙar Inshorar Lafiya Ba Bisa Ka’ida Ba

Wadannan matakai sun haɗa da kare mata daga cin zarafi, samar da damammaki a fannin ilimi da sana’a, da kuma sauya wasu tsofaffin al’adu da ke hana su ci gaba.

Ina Najeriya Ta Kwana?

Najeriya na daga cikin kasashen da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya, amma tambayar da ake yi ita ce: Shin an samu ci gaba ko kuwa har yanzu mata na fama da irin matsalolin da ake son kawarwa?

Advertisement

A bangaren zamantakewa, ana iya cewa akwai ci gaba a yadda ake kallon mata da rawar da suke takawa a al’umma. Blessing Mato, wata ‘yar kasuwa kuma mai fafutuka kan kare hakkin mata, ta ce har yanzu akwai al’adu da ke hana mata samun cikakken ‘yanci.

“Sau da yawa ana ganin cewa dole mace ta zauna a gida ta kula da iyali maimakon ta fita ta yi aiki. Me zai hana mace ta kula da gidanta kuma ta yi sana’a ko aikin da take so? Ya kamata a sauya wannan tunani,” in ji Mato.

Sai dai tana mai jaddada cewa an samu cigaba, musamman a yadda maza ke tallafa wa mata a rayuwar yau da kullum. Haka kuma, an fara ganin sauyi a fannonin ilimi, kasuwanci, siyasa, da kuma aikin gwamnati, inda mata ke samun damar cimma burinsu.

 

Kalubalen Da Suka Rage

Duk da wadannan ci gaban, har yanzu akwai wasu matsaloli da ke bukatar a yi aiki akansu na Ranar Mata. Har yau, albashin maza na fin na mata yawa a wasu wuraren aiki, kuma akwai mace-macen aure saboda mace ta nemi ilimi ko kuma ta samu ci gaba a rayuwa. Bugu da kari, tsoron abin da al’umma za ta ce kan wasu matakai na ci gaban mata na hana wasu mata yin abubuwan da suke so.

Advertisement

A yayin da duniya ke karrama wannan rana, yana da kyau gwamnatoci, kungiyoyi, da al’umma baki ɗaya su ƙara azama wajen tabbatar da kare hakkin mata, domin hakan ne kawai zai tabbatar da ingantacciyar al’umma mai cike da adalci da daidaito ga kowa.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending