News
Ƴan Bindiga Sun Shiga Hannun Jami’an Tsaro A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan bindiga da suka yi kuste a jihar da nufin aikata mummunar manufa, lamarin da ya kai ga cafke su bayan da asirinsu ya tonu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar, 08 ga watan Maris, 2025.
Yayin da Duniya Ke Karrama Ranar Mata: Ina Aka Kwana a Batun Kare Hakkokinsu?
Ya kara da cewa ana ci gaba da bincike, kuma za a fitar da karin bayani nan gaba kan yadda aka kama su da kuma irin laifuffukan da ake zargin su da aikatawa.
Hukumar ‘yan sanda ta jaddada kudirinta na ci gaba da yaki da aikata laifuka tare da tabbatar da tsaro a Kano da ma Najeriya baki daya.
Advertisements
