News
Ƴan Sanda Sun Cafke Hatsabiban Ƴan Bindiga 4 A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutum hudu da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci, tare da kwato makamai da wasu kayayyaki masu hadari. An kama su ne a kan titin By-pass, unguwar Hotoro, a karamar hukumar Nasarawa, bayan samun sahihan bayanan sirri.
A cewar rahoton ‘yan sanda, an kai samamen ne a ranar 6 ga Maris, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, inda aka damke:
Shukurana Salihu (25)
Rabi’u Dahiru (35)
Ya’u Idris (30) daga Katsina
Muktar Sani daga Yandodo, Hotoro
Bayanai sun nuna cewa an samu makamai a hannunsu, ciki har da bindigogi uku kirar gida, takubba biyu, harsasai 12, gidan alburusai uku, wukake hudu, da wayoyi hudu.
Jami’an tsaro sun bayyana cewa wannan na daga cikin kokarin dakile ayyukan bata-gari da kuma hana satar motoci a jihar.
A wani samame daban, rundunar ta kama wasu mutum uku da ake zargi da satar mota, tare da kwato motocin da suka sace.
Kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci jama’a su ci gaba da bayar da hadin kai da bayar da bayanai domin tabbatar da tsaro. An tabbatar da cewa da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.
