News
Mazauna Garuruwan Alazawa Da Gazan Sun Gudanar Alkunutu Bisa Matsalolin Da Suka Dabaibaye Yankin
Mazauna garuruwan Alazawa da Gazan da ke karamar hukumar Kiru a Jihar Kano sun dukufa cikin addu’o’i da sallar Alkunutu, suna neman taimakon Allah bisa matsalolin da suka dabaibaye su.
A cewar mazauna yankin, matsalar rashin hanyoyi da rushewar gadoji guda uku sun jefa su cikin mawuyacin hali, inda zirga-zirga ta zama mai wahala.
Mazauna Garuruwan Alazawa Da Gazan Sun Gudanar Alkunutu Bisa Matsalolin Da Suka Dabaibaye Yankin
Baya ga haka, babu asibiti da zai kula da marasa lafiya, yayin da makarantu na firamare da sakandire suka lalace, lamarin da ke barazana ga ilimin ‘ya’yansu.
Dalilin haka ne ya sa su ka gudanar da addu’o’i, suna rokon Allah ya karkato da zukatan shugabanni don su kawo musu dauki tare da aiwatar da ayyukan da za su rage musu radadin wahalar da suke ciki.
EXPRESS RADIYO ta ruwaito cewa Mazauna yankin sun bukacin Gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar mataki domin inganta rayuwar al’ummar yankin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
