News
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Kauyuka Biyar A Kaduna
Yan bindiga sun yi wa wasu kauyuka biyar a karamar hukumar Kachia ta Jihar Kaduna dirar mikiya, inda suka tilasta wa mazauna tserewa tare da kona wata mota da babur guda.
Kauyukan da harin ya shafa sun hada da Unguwan Tauka, Unguwan Lalle, Sannu da Zuwa, Tsauni Dodo da Dandauka. Baya ga haka, ‘yan bindigar sun kai farmaki a wani yankin Fulani da ke Kubuwo, inda suka sace wasu matasa makiyaya guda uku.
Gobara Ta Lakume Rayuka 7, Ta Haddasa Asarar Naira Miliyan 50 A Kano
Wani shugaban yankin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe shida na yamma bayan da ‘yan bindigar suka tsere daga farmakin da sojoji suka kai a dajin Kurutu-Azara. Rundunar ‘yan sandan yankin ta tabbatar da aukuwar harin amma bata bayyana yawan asarar rayuka ko jikkata ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
