News
Jami’an Yan Sanda Sun Gano Gawar Almajiri da Aka Cire Masa Kai A Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da tsintar gawar wani almajiri dan shekara 14 mai suna Bashir Adamu, dalibin Malam Musa Wada, a kauyen Jikas-Dabaja da ke karamar hukumar Gwaram.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Shi’isu Lawan Adam, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunar ta’asa, inda ya bayyana cewa an gano gawar yaron a gefen hanya bayan ya bata na tsawon kwanaki biyu.
Har yanzu ba a gano wanda ke da hannu a wannan aika-aika ba, amma hukumomi sun fara bincike don gano masu hannu a lamarin.
Wannan kisan gilla ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da fargaba, inda jama’a ke kira ga hukumomi da su gaggauta daukar matakan kare rayukan ‘ya’yansu.
-
News7 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
