Connect with us

News

Kotu Ta Daure Matashi Saboda Ji Wa Makwabcinsa Rauni Da Almakashi A Kano

Published

on

Kotu Ta Daure Matashi Saboda Ji Wa Makwabcinsa Rauni Da Almakashi A Kano

 

Kotun Shari’a dake Kano ta yanke wa wani matashi mai shekaru 29, Abduljabar Nura, hukuncin zaman gidan gyaran hali bayan an kama shi da laifin ji wa makwabcinsa rauni da almakashi a bayan sa.

Advertisement

Dan sandan da ya shigar da karar, Zahradeen Abubakar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a unguwar Fagge, inda Nura da makwabcinsa, Haruna Kasim, suka samu sabani kan batun takardar kudin wutar lantarki.

Cacan-bakin da suka yi ya rikide zuwa fada, wanda ya kai ga Nura ya daba wa Kasim almakashi a bayan sa.

Advertisement

Ango Da ’Yar Uwar Amarya Sun Rasu Mintuna 30 Kafin Daurin Aure A Bauchi

Abubakar ya ce ‘yan sanda sun samu labarin faruwar lamarin bayan Kasim ya kai rahoto a ofishinsu dake Fagge a ranar 28 ga Fabrairu. An tuhumi Nura bisa laifin da ya saba wa sashe 158 da 165 na dokar Penal Code ta jihar Kano, kuma ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Alkalin kotun, Malam Umar Lawal-Abubakar, ya yanke hukuncin daure Nura a gidan gyaran hali dake Goron Dutse har zuwa ranar 15 ga Afrilu, lokacin da za a yanke masa hukunci na ƙarshe.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending