News
An Rushe Gine-Gine A Badalar ‘Dan Agundi A Kano
A daren jiya, wasu gine-gine guda biyu da ke yankin Badalar ‘Dan Agundi, Kano, sun fuskanci rusau da ba a bayyana masu alhaki ba. Shaidu sun ce jami’an tsaro dauke da bindigu sun kama mai gadin wajen tare da sanya masa ankwa kafin fara aikin rusau.
AREWA RADIO ta ruwaito cewa filayen da aka rushe na daga cikin wuraren da ake takaddama a kotu tsakanin masu ginin da Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano.
Gwamnatin Kano Ta Neman Hadin Gwiwa Da Saudiyya Wajen Gina Cibiyar Maganin Zuciya da Fitsari
Tun farkon mulkinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna shirin rushe gine-ginen da aka yi a yankunan Badalar ‘Dan Agundi zuwa Kofar Fanfo, inda aka ce tsohuwar gwamnatin Kano ce ta raba filayen.
Har yanzu babu wata hukuma da ta fito fili ta dauki alhakin rushewar, amma al’umma sun nuna damuwa kan yadda aka gudanar da aikin a cikin dare, lamarin da ke kara dagula rikicin mallakar wuraren.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
