Connect with us

News

Majalisar Wakilai Za Ta Haramtawa Masu Shekaru Sama da 60 Tsayawa Takara

Published

on

takara

Majalisar Wakilan Najeriya ta tsallake karatu na biyu kan kudurin dokar da ke neman hana ‘yan takarar shugaban kasa da gwamna masu shekaru sama da 60 shiga takara.

A zaman majalisar na yau Alhamis, an amince da kudurin bayan gabatarwar dan majalisa, Hon. Ikeagwuonu Ugochinyere, wanda ke neman a yi garambawul ga wasu sassa na kundin tsarin mulkin kasa na 1999.

Titin Jirgin Ƙasa Daga Legas Zuwa Kano Zai Fara Aiki —Hukumar NRC

Rahotanni sun bayyana cewa idan kudurin ya tsallake karatu na uku, kuma shugaban kasa ya sanya hannu a kai, zai canza tsarin cancantar tsayawa takara a kasar.

Daga cikin muhimman sauye-sauyen da kudurin ya kunsa sun hada da:

Duk wanda ya haura shekaru 60 ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa ko gwamna ba.

Dole ne duk wani dan takara ya mallaki digiri na farko a bangaren da ya fi kwarewa, a matsayin mafi karancin matakin ilimi.

Advertisement

Kudurin ya bukaci a yi gyara a sashe na 131 na kundin tsarin mulkin kasa don iyakance shekarun takarar shugaban kasa, da sashe na 177 don gwamnonin jihohi.

Baya ga wannan kuduri, majalisar ta kuma amince da wasu kudurori daban-daban da suka shafi cigaban Najeriya.

Sai dai Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Jam’iyyun PDP, CUPP da SDP Sun Yi Allah wadai da matakin da Majalisar Wakilan Najeriya ta dauka na kakaba iyakar shekaru ga masu neman mukaman shugaban kasa da gwamna a kasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending