News
SANKARAU: Mutum 60 Sun Rasa Rayukansu A Kebbi, Barazanar Yaduwar Cutar Na Karuwa
Cutar sankarau ta ci gaba da yaduwa a Najeriya, inda ta yi sanadin rasuwar mutum 60 a jihar Kebbi kadai, kamar yadda kungiyar likitoci marasa iyaka (MSF) ta bayyana.
Teresa Krug, jami’ar yada labarai na MSF, ta ce cutar na bazuwa kamar wutar daji a Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman a jihohin Sokoto da Kebbi. A cewarta, jihar Kebbi ta fi shan wahala a bana, inda cutar ta bullo a kananan hukumomin Gwandu, Jega, da Aliero.
Yaro Dan Shekara 4 Ya Kira ‘Yan Sanda Saboda Ice Cream Da Mahaifiyarsa Ta Shanye
A cewar MSF, fiye da marasa lafiya 500 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Kebbi, yayin da yawan mace-macen ya kai 60.
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta tabbatar da mutuwar mutum 74 daga cutar a jihohi 21 da Abuja. Jihohin Katsina, Sokoto, da Kebbi na cikin wuraren da cutar ta fi kamari.
Sani Datti, jami’in hulda da jama’a na NCDC, ya bayyana cewa hukumar ta tura jami’anta domin dakile yaduwar cutar a yankunan da abin ya fi shafa.
A cikin shekarar 2025 kadai, mutane 807 ake zargin sun kamu da sankarau, inda cutar ta haddasa mutuwar 74 daga cikinsu. Jihohin da suka fi fuskantar barazanar cutar sun hada da Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Yobe, Gombe, Adamawa, Borno, da wasu yankuna har da Abuja.
A yayin da yaduwar cutar ke kara kamari, kungiyar MSF ta koka kan yadda marasa lafiya ke samun wahalar samun magani, musamman a jihohin Kebbi da Sokoto.
Bukar Galtimari, wani likita a kungiyar MSF, ya bayyana cewa cutar ana iya warkewa daga ita idan aka samu kulawar gaggawa. Sai dai, rashin garzayawa asibiti na kara ta’azzara matsalar.
“Mutane da dama na fuskantar alamun cutar kamar ciwon kai mai tsanani, zazzabi, amai, suma, makalewar wuya, da rashin iya jure haske,” in ji shi.
Kungiyar MSF ta bukaci hadin gwiwar gwamnatoci domin samar da magunguna da yin rigakafi ga jama’a, musamman a jihohin Sokoto da Kebbi.
A nata bangaren, gwamnatin jihohin Kebbi da Sokoto ta bayyana cewa tana shirin fara yi wa jama’a allurar rigakafi daga watan Afrilu domin dakile yaduwar cutar.
