Connect with us

News

Gwamnan Kano: A Bayyana Masu Hannu a Kisan ‘Yan Jiharmu a Edo

Published

on

FB IMG 1743429065225

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci gwamnatin Jihar Edo da ta fito da bayani kan wadanda suka aikata kisan gillar da ya rutsa da mafarauta 16 a garin Uromi, yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida domin bukukuwan Sallah.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jaje da takwaransa na Edo, Monday Okpebholo, ya kai Kano don nuna alhini bisa wannan mummunan lamari.

Advertisement

‎Zazzabin Lassa: Cutar Ta Yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku  ‎ ‎– Hukumar NCDC

“Ina kira ga Gwamnan Edo da ya tabbatar da cewa ba wai kawai a kama wadanda suka aikata wannan aika-aika ba, har ma a yi holensu ga jama’a domin duniya ta gani,” in ji Gwamnan Kano.

 

Advertisement

A nasa bangaren, Gwamnan Edo ya tabbatar da cewa an riga an kama mutum 14 da ake zargi da hannu a lamarin, kuma ana ci gaba da bincike a Abuja. Ya kuma tabbatar da cewa Shugaban Kasa ya dauki matakin tabbatar da adalci.

Wannan kisan gillar ya tayar da hankula, yayin da ake ci gaba da bukatar a dauki mataki don tabbatar da cewa irin wannan ta’addanci bai sake faruwa ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending