News
NBC Ta Haramta Saka Waƙar “Tell Your Papa” Ta Eedris Abdulkareem: Sako Mai Cike Da Caccaka Zuwa Ga Seyi Tinubu
Hukumar da ke kula da kafafen yaɗa labarai a Najeriya (NBC), ta bayar da umarnin dakatar da saka waƙar “Tell Your Papa” ta shahararren mawaki Eedris Abdulkareem a gidajen rediyo da talabijin.
Waƙar, wadda aka saki a ranar Lahadi, ta ƙunshi sako kai-tsaye zuwa ga ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, inda Eedris ke roƙon shi da ya gaya wa mahaifinsa, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauki matakin gaggawa wajen magance matsalolin tattalin arziki da ke addabar ‘yan Najeriya.
Sai dai a wata sanarwa da daraktar kula da kafofin yaɗa labarai, Susan Obi, ta fitar a ranar Alhamis, NBC ta bayyana waƙar a matsayin wacce ba ta dace da ƙa’idojin hukumar ba.
“Waƙar na ɗauke da abun da ya saɓa da sashe na 3.1.8 na kundin dokar yaɗa labarai ta ƙasa, kuma ta na cikin jerin waƙoƙin da aka haramta saka su ga jama’a,” in ji sanarwar.
NBC ta gargadi kafafen yaɗa labarai da su guji saka waƙar, tana mai kira da su mutunta ƙa’idojin da ke jagorantar harkar, tare da haɗin kai wajen tabbatar da bin doka.
Waƙar ta haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra’ayoyinsu kan matakin da NBC ta ɗauka.
