News
‘Yan Majalisar Arewa Maso Gabas Sun Zargi Gwamnatin Shugaba Tinubu Da Wariya
Yan majalisar tarayya daga yankin Arewa maso Gabas sun bayyana ƙin jin daɗinsu kan cire yankin daga cikin jihohin da za su amfana da shirin Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ), wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ci gaban duniya.
A wata ganawa da manema labarai bayan wani taron gaggawa a Abuja, North-East Caucus – wato ƙungiyar ‘yan majalisa daga jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe – ta nuna damuwa kan yadda yankin, wanda ke taka muhimmiyar rawa a ɓangaren noma da kiwo, ya kasance a gefe wajen aiwatar da wannan babban shiri.
NDLEA Ta Kama Mutane 22, Ta Kwato Miyagun Kwayoyi Da Makamai A Kano
Sanata Danjuma Goje, mai wakiltar Gombe ta Tsakiya kuma shugaban ƙungiyar, ya bayyana cewa abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya da haɗin gwiwar African Development Bank (AfDB), Islamic Development Bank (IsDB) da kuma International Fund for Agricultural Development (IFAD) suka ware dala miliyan $530 don aiwatar da SAPZ ba tare da sanya ko ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Gabas ba.
A cewar Goje, a ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da zagaye na farko na shirin a jihar Kaduna. Sai dai, cikin jihohi bakwai da birnin tarayya (FCT) da suka ci gajiyar shirin, babu ɗaya daga Arewa maso Gabas.
> “Jihohin Kaduna, Kano, Ogun da Oyo sun samu yankuna biyu-biyu, yayin da Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya suka samu yanki guda-guda. Amma Arewa maso Gabas ba ta samu ko ɗaya ba,” in ji Goje.
Ya bayyana cewa hakan ya saba da alƙawarin haɗin kai da ci gaba da gwamnatin Tinubu ke yi a bainar jama’a, musamman duba da rawar da yankin ke takawa wajen samar da abinci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
> “Yankinmu na da ɗimbin albarkatun noma da kiwo, kuma yana da matuƙar tasiri ga GDP na ƙasa. Don haka, gazawar sanya mu a cikin wannan shiri mai muhimmanci ya jefa mu cikin damuwa da mamaki,” in ji shi.
Sanata Goje ya ƙara da cewa manufar shirin SAPZ ita ce haɗa manoma da masana’antu, rage asarar amfanin gona bayan girbi, da kuma bunƙasa rayuwar al’umman karkara. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta saka yankin Arewa maso Gabas cikin shirin domin tabbatar da adalci da haɗin kai.
> “Wannan shiri na fifiko na shugaban ƙasa ne, kuma bai kamata a bar yankin da ke fama da kalubale na tsaro da koma-baya a cigaba ba,” in ji Goje.
North-East Caucus ta bayyana cewa halin da ake ciki na nuna gazawar gwamnati wajen tafiyar da shirinta bisa gaskiya da adalci, lamarin da ka iya ƙara fargaba da rashin yarda daga al’umman yankin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
