Connect with us

News

Barazanar Ficewar Meta Ba Za Ta Hana Hukuncin Da Aka Zartar Ba —FCCPC

Published

on

Facebook (1)

Hukumar kare hakkin mai Saye da Ingancin Fasaha (FCCPC) ta ce barazanar kamfanin Meta na ficewa daga Najeriya ba zai hana hukuncin da aka zartar a kansa ba.

A cikin wata sanarwa da Darektan Hulda da Jama’a na hukumar, Mista Ondaje Ijagwu, ya fitar ranar Asabar, FCCPC ta bayyana cewa barazanar da WhatsApp ta yi na dakatar da ayyukanta a Najeriya wata dabara ce kawai don tada jijiyar wuya da neman jin kai daga al’umma.

India Ta Hana Shigo Da Kaya Daga Pakistan

Sanarwar ta biyo bayan wata wasika daga Meta da ta ce ana iya tilasta musu rufe Facebook da Instagram a Najeriya domin gujewa hukuncin da hukumar za ta aiwatar.

A baya-bayan nan, hukumar ta ci Meta tarar dala miliyan 220 a ranar 19 ga Yuli, 2024, bisa laifin karya dokokin bayanan sirri da kuma dokar kare masu amfani da kayayyaki.

Meta, wadda ita ce mai WhatsApp, ta fuskanci zargi na:

Hana ’yan Najeriya ikon sarrafa bayanan kansu

Advertisement

Raba bayanan masu amfani da su ba tare da izini ba

Nuna wariya ga ’yan Najeriya idan aka kwatanta da masu amfani a wasu kasashe

Tilasta amfani da manufofin sirri da ba su da adalci.

A ranar 25 ga Afrilu ne Kotun Tattaunawa kan Gasa da Kare Masu Amfani da Kaya ta tabbatar da sahihancin tarar da FCCPC ta kakabawa Meta.

 

Sanarwar ta kara da cewa Meta ba ta taba yin barazana da ficewa daga wasu kasashen da aka ci ta tara ba, ciki har da Texas, inda aka ci ta dala biliyan 1.5, da Tarayyar Turai, inda aka ci ta dala biliyan 1.3 saboda irin wannan laifi.

Advertisement

Hakazalika, Meta ta fuskanci hukunci a kasashen Indiya, Koriya ta Kudu, Faransa da Ostiraliya, amma ba ta taɓa yin barazanar ficewa daga wadancan kasashe ba.

“Barazanar da Meta ke yi ba za ta sauya matsayar FCCPC ba, kuma ficewarsu daga Najeriya ba zai hana aiwatar da hukuncin doka da aka yanke musu ba,” in ji hukumar.

FCCPC ta ce ta kuduri aniyar ci gaba da kare hakkin ’yan Najeriya da tabbatar da adalci a kasuwar zamani, kamar yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba.

 

 

 

Advertisement

CHANNELS TV

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending