News
RMAFC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sake Duba ’Yancin Kananan Hukumomi
Hukumar Rarraba Arzikin Ƙasa (RMAFC) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sake duba yadda ake tafiyar da kuɗaɗen kananan hukumomi 774 a faɗin ƙasar nan.
Hukumar ta kuma ce akwai buƙatar a duba yadda ake aiwatar da sabuwar Dokar Man Fetur (PIA) domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rarraba arzikin ƙasa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar bayan kammala wani taron horo na kwanaki uku da aka gudanar a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom.
Sanarwar, wadda Shugaban Hukumar RMAFC, Dr. Muhammed Shehu, da Sakatare, Injiniya Joseph Okechukwu Nwazeb suka sanya wa hannu, ta bayyana cewa ya zama dole a riƙa biyan kuɗaɗen kananan hukumomi kai tsaye daga Asusun Tarayya ba tare da tsoma bakin gwamnatocin jihohi ba.
“Hakan zai ba kananan hukumomi damar cin gashin kansu da kuma gudanar da ayyukan raya ƙasa cikin sauƙi,” in ji sanarwar.
Hukumar ta kuma nemi a sauya Sashe na 162(2) na Kundin Tsarin Mulki, domin sanya lokaci na musamman da Shugaban Ƙasa zai gabatar da tsarin rarraba kuɗaɗen shiga na RMAFC ga Majalisar Ƙasa.
A cewar hukumar, hakan zai taimaka wajen ganin an raba arzikin ƙasa cikin lokaci da kuma bisa gaskiya da adalci.
Game da Dokar Man Fetur kuwa, RMAFC ta nemi a faɗaɗa kwamitin gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), domin haɗa wakilai daga jihohi da kananan hukumomi, da kuma wakilin Babban Bankin Najeriya (CBN).
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
