Connect with us

News

ISWAP Ta Kai Hari Sansanin Sojoji A Yobe

Published

on

0bef93bb 5576 42fe b7df 28a46af5224a

Mayaƙan ISWAP sun kai hari a wani ɓangare na sansanin sojoji na 27 Brigade da ke garin Buni Gari, ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe, da misalin ƙarfe 12 na daren Juma’a.

Wannan hari ya auku ne kwanaki biyu bayan taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas da aka gudanar domin tattauna matsalolin tsaro, talauci da gyaran hanyoyin mota a yankin.

Advertisement

Pakistan Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Yayin Da Rikici Da Indiya Ke Kara Tsananta

Wani jami’in tsaro da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mayaƙan sun kai hari kan sansanin sojoji da ke kusa da Buni Yadi, inda ake da Makarantar Sojoji ta Musamman.

Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun fara harbe-harbe kafin su ƙone wasu gine-gine da ke cikin sansanin, da wasu mallakar al’umma.

Advertisement

Sai dai dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan tare da fatattakar su.

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da harin a shafinta na sada zumunta ranar Asabar.

Advertisement

Wata majiya daga sahun leƙen asiri ta shaida wa LEADSHIP cewa jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar masu farauta da ‘yan sa kai sun yi artabu da mayaƙan na tsawon awa ɗaya, inda suka yi nasarar kashe da dama daga cikinsu.

Kawo yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan adadin asarar rayuka ko irin barnar da aka yi ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending