News
Alert Ɗin Bogi Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Matasa Uku A Kano
Wasu matasa uku sun rasa rayukansu a wani kududdufi da ke unguwar Gwazaye a karamar hukumar Kumbotso, Jihar Kano, yayin da suke yunkurin cafke wani da ake zargi da damfarar jama’a ta hanyar aika musu da alert ɗin bogi.
Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ce ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta samu kiran gaggawa daga wani mutum mai suna Garba Sani, cewa wasu sun faɗa rijiya kusa da hanyar Ring Road, Dorayi Babba.
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce da jami’ansu suka isa wurin, sun tarar da cewa matasa biyu – Saifullahi Muhammad da Halifa Abdullahi – sun bi wani mutum daga kasuwar Kofar Ruwa, bisa zargin ya yaudarar su ta hanyar aika musu da alert ɗin bogi bayan sayayya.
Ya ce mutumin da suka bi ya faɗa cikin kududdufin, su kuma suka shiga don cafkarsa, amma gaba ɗayansu uku suka nutse.
Bayan an ciro su daga cikin ruwan, an kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
An mika gawarwakin ga ’yan sanda na ofishin Kuntau, ƙarƙashin Insfekta Halifa Muhammad domin ci gaba da bincike.
Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin matasan da suka mutu ya ce, mutumin da suka bi yana da dabi’ar tura alert ɗin bogi a kasuwanni bayan karɓar kaya daga hannun mutane.
Al’ummar yankin sun nuna bacin rai game da yadda matsalar damfara da tura alert bogi ke ƙaruwa a Kano, inda suka bukaci hukumomi da su tsaurara mataki domin hana yawaitar wannan muguwar dabi’a.
