Connect with us

News

RUWAN SHA YA ZAMA BARAZANA: Ƙauyukan Da Mutane, Jakuna Da Karnuka Ke Shan Ruwa Waje Ɗaya A Kano

Published

on

IMG 20250526 WA0042

Mutane da dabbobi na cikin matsanancin halin rashin ruwa mai tsafta a kauyukan Munari da wasu kauyuka a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Warawa, jihar Kano. Wannan matsala ta tilasta wa mutane, jakuna da karnuka shan ruwa a wuri ɗaya, lamarin da ke haifar da barazana ga lafiyar jama’a.

Kauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Munari, Baruge, Maraya Wuta, Madarin Fulani, Kwalele, Dan Tuyi da Gana Ka Kunda, inda al’umma ke amfani da rijiyoyi ko tafkuna ɗaya domin samun ruwa, duk da haɗarin dake tattare da hakan.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Ware Kuɗi Mai Yawa Don Gyara Gadan Bayan Gobarar Masallaci

Wani mazaunin kauyen Munari ya bayyana cewa, “Ruwan da muke sha, dabbobi da mutane ne ke haɗuwa a wajen. Amma ba mu da wani zaɓi, sai mu sha shi duk da cewa yana da haɗari sosai.”

Ya kara da cewa, wannan matsala ta ci gaba da damun al’umma na tsawon shekaru ba tare da wani ingantaccen mataki daga gwamnati ba. Rashin samun ruwa mai tsafta ya hana yara mata damar zuwa makaranta, domin suna fita tun da asuba don neman ruwa, sannan idan sun dawo suna gajiya sosai har ba su iya gudanar da sauran ayyukansu ba.

Advertisement

“Yara mata yanzu basa zuwa makaranta. Duk safiya sai sun fita neman ruwa. Idan sun dawo kuma sun gaji sosai, hakan na shafar karatunsu,” in ji wani mazauni

Rahotanni sun nuna cewa amfani da ruwan da ba shi da tsafta a yankin yana haifar da yaduwar cututtuka irin su amai, gudawa da ciwon ciki, wanda ke zama babban kalubale ga lafiyar al’umma da ci gaban yankin gaba ɗaya.

Advertisement

A saboda haka, al’ummar yankin sun roƙi gwamnatin jihar Kano, tare da haɗin gwiwar gwamnati ta tarayya da ƙungiyoyin agaji, da su hanzarta ɗaukar matakan samar da rijiyoyi ko bututun ruwa domin kawo ƙarshen wannan matsala mai tsawo.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, hukumomin da abin ya shafa basu ba da wani bayani kan matakan da za su ɗauka ba. Haka kuma, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar Kano, Dr. Dahir M. Hashim, bai amsa kira ko saƙon jaridar INDA RANKA ba domin jin ta bakin sa kan wannan matsala.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending