Connect with us

News

Kotun  Ta Yanke Wa Wani Magidanci Mai Shekaru 56 Hukuncin Daurin Rai-Da-Rai

Published

on

Kotu

Babbar Kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a Ado-Ekiti, ta yanke wa wani magidanci mai shekaru 56 hukuncin daurin rai-da-rai bisa samunsa da laifin yi wa agolarsa mai shekaru 14 fyaɗe.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan gurfanar da wanda ake tuhuma a gabanta a watan Oktoban shekarar 2024, inda aka bayyana cewa laifin ya faru a cikin gida, watanni bakwai da suka gabata.

Advertisement

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Grow Homes Estate, Sun Yi Garkuwa Da Mutane Biyu

Mai gabatar da ƙara, Julius Ajibare, ya gabatar da shaidu guda shida da suka tabbatar da cewa wanda ake tuhuma — mijin mahaifiyar yarinyar — ya aikata laifin fyade.

 

Advertisement

Haka kuma, an gabatar da sakamakon binciken likita da wasu ƙarin hujjoji da suka tabbatar da sahihancin zargin da ake masa.

Ko da yake lauyan wanda ake tuhuma, Olajide Adedeji, ya gabatar da shaida guda ɗaya domin kare wanda yake wakilta, kotun ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai bayan ta gamsu da shaidu da hujjojin da aka gabatar mata.

Advertisement

Hukuncin ya jaddada kudirin kotuna wajen yaki da aikata fyaɗe musamman ga ƙananan yara, da kuma tabbatar da kariya ga marasa galihu cikin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending