News
Amurka na nuna damuwa kan China za ta iya taimakawa Rasha da kayan yaki
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Fadar White House ta nuna damuwa matuƙa kan cewa akwai yiwuwar China za ta iya aika wa Rasha da makamai waɗanda za a iya amfani da su domin a yaƙi Ukraine.
A wani taron manema labarai a Amurka, sakatariyar watsa labarai ta fadar White House Jen Psaki, cewa ta yi ƙin fitowar da Chinar ta yi fili ta yi Allah wadai da Rasha ya saɓa wa duk wasu abubuwan da Chinar take tunƙaho da su.
Ms Psaki tace a idan kuka yi duba da abubuwan da suka faru a makonnin da suka gabata, za ku ga Chinar ta ƙaurace wa jefa ƙuri’a a kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ana sa ra a yau Shugaban Amurkar Joe Biden zai tattauna da takwaransa na China Xi Jing Ping ta waya.
-
News1 day ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News5 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News3 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
