Connect with us

News

Shugabar Tanzania ta cika shekara guda a ofis

Published

on

Advertisements
ads
  1. Daga maryam bashir musa

 

 

.

A wannan karshen makon ne tsohuwar mataimakiyar shugaban Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta zama mace ta farko da ta zama shugaban kasar.

Duk da cewa ita ce shugabar wata kasar Afrika tilo mace, amma ba ta son ana kiranta da wani suna a hukumance bayan sunan da take so “Mama Samia” ko kuma Samia in ji ta.

An rantsar da ita ne lokacin da ake tsaka da fama da annobar korona, a watan Maris din bara bayan wanda ta gada shugaba Magufuli ya yi mutuwar fuju’a a ofis.

Tun wannan lokacin take son haskaka Tanzania a idon duniya. Ciki har da fim din “Royal Tour” da za a haska nan da watan Afrilun wannan shekarar da muke ciki.

Advertisement

Mama Samia ta zagaya kusan sassan kasar baki daya, tare da wasu masu shirya fim na Amurka domin nuna musu abinda kasar ke da shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending